◐ Shell
reader mode source ↗

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 15/06/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Litinin 15 ga watan Yunin 2026.

Skip Bidiyo and continue reading
  • xxx
    Bidiyo, Abin da ya sa wasu ke alaƙanta ni da ƴan fashin daji - Matawalle, Tsawon lokaci 12,20
  • xxx
    Bidiyo, Gaskiyar abin da ya sa zan yi wa Obi mataimaki - Kwankwaso, Tsawon lokaci 11,38
  • xxx
    Bidiyo, Yadda aka kwaso yan Najeriya daga Afirka ta Kudu, Tsawon lokaci 3,17
  • Arsenal
    Bidiyo, 'Da muka lashe Premier sai da iyalina ta haƙura da ni', Tsawon lokaci 2,21
  • xxx
    Bidiyo, Arsenal ko PSG? Wa zai lashe Champions League na bana, Tsawon lokaci 2,01
  • xxx
    Bidiyo, Tareni: Daɗaɗɗiyar al'adar sarrafa naman layya a ƙasar Hausa, Tsawon lokaci 2,44
  • xxx
    Bidiyo, Saƙon Barka da Sallah a harsunan Afirka, Tsawon lokaci 0,43
  • xxx
    Bidiyo, 'Na daɗe ina haƙuri da Abba Kabir Yusuf', Tsawon lokaci 11,27
  • Kutama
    Bidiyo, Yadda kasuwanni ke ci gabanin bukukuwan sallah, Tsawon lokaci 1,29
  • xxx
    Bidiyo, 'APC ba ta bi ƙa'idar zaɓen fitar da gwani ba' , Tsawon lokaci 1,29
  • Sadis Buba
    Bidiyo, Ba zan janye daga takara ba - Buba, Tsawon lokaci 5,11
  • Pantami
    Bidiyo, 'Abin da ya sa na sulhunta El-Rufai da Uba Sani a maƙabarta', Tsawon lokaci 2,10
  • xxx
    Bidiyo, Mene ne matsayin Ganduje a siyasar Kano?, Tsawon lokaci 1,35

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida, Muslim Muhammad Yusuf da Usman MINJIBIR

  1. An saki matar Janar Rabe da ya rasu a hannun ƴan bindiga - Sojoji

    Sojoji

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar sojin Najeriya ta ce ta ceto matar Janar Rabe Abubakar mai ritaya da ya rasu a hannun ƴan bindiga a jihar Katsina.

    A wata sanarwa da daraktan yaɗa labaran rundunar Samaila Uba ya fitar, ya ce dakarunsu sun ceto Amina Abubakar bayan ɓarin wuta da ƴan bindiga, inda har ta kai ga ƴan bindigar sun harbi matar kafin su sake ta, su tsere cikin daji.

    "Tana samun kulawa yanzu haka a asibitin sojoji, kuma tana samun sauƙi," in ji sanarwar.

    Iyalan marigayin sun tabbatar wa BBC cewa sun samu labarin sakin mahaifiyar tasu wadda aka kama su tare.

    Kamar yadda BBC ta samu labari daga ɗaya daga cikin ƴaƴansa, sun ce ba su yi ido biyu da ita ba amma an shaida musu cewa yanzu haka suna kan hanyar zuwa gida inda ake dakon isowarsu.

    Sun ce sojoji ne suka taho da mahaifiyar tasu, inda suka buƙaci su shirya mata kayanta kafin su ƙarasa.

  2. Za a buɗe Mashigar Hormuz ranar Juma'a - Amurka

    Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Jami'an fadar White House sun ba da ƙarin bayani kan yarjejeniyar Iran da Amurka.

    Sun ce za a buɗe Mashigar Hormuz a ranar juma'a, ranar da za a sanya hannu kan yarjejeniyar a hukumance a Geneva, inda jirage za su fara wucewa.

    Ana sa ran fara tattauna wa kan batun da ya shafi shirin makamin nukiliyar Iran a wannan makon, yayin da za a ci gaba da duba yiwuwar janye takunkumi da sakin kuɗaɗen Iran da aka riƙe, kuma hakan ya danganta da yadda Iran ta nuna shirinta na aminta da yarjejniyar.

    Jami'an sun ce Lebanon na cikin yarjejeniyar tsagaita wutar, amma janyewar dakarun Isra'ila ba ya cikin yarjejeniyar.

  3. Hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ya ƙaru zuwa kashi 15.93

    Hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ya ƙaru zuwa kashi 15.93

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar Kididdiga ta Najeriya (NBS) ta ce hauhawar farashin kayan masarufi a Najeriya ya ƙaru zuwa kashi 15.93 a watan Mayun 2026.

    NBS ta sanar da alƙaluman ne a ranar Litinin, wanda shi ne karo na uku a shekarar 2026.

    Hukumar ta ce hauhawar farashin kayan abinci a watan Mayu ya kai kashi 16.96%, saɓanin yadda yake a 16.68% a watan Afrilu.

    Yawancin kayan abincin da hauhawar farashin ya shafa su ne: Albasa, masara, hatsi, rogo, fulawa, dankali, wake, tumatur, doya, citta da sauransu.

    NBS ta ce hauhawar farashin ya ƙaru sosai a jihohin Adamawa da ke da 29.62% da Kwara da ke 28.47% da Kuma Rivers da ke 28.40%.

    Sai dai an samu saukar farashin a jihohin Borno da Taraba da Bayelsa.

  4. Rundunar Sojin Najeriya ta ƙaddamar da hare-hare kan maɓoyar ƴan bindiga a Katsina

    Army

    Asalin hoton, Army/X

    Rundunar Sojin Najeriya ta ce ta ƙaddamar da wasu zafafan hare-hare kan ƴan bindiga a wasu yankuna na jihar Katsina da ke arewa maso gabashin ƙasar.

    Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan mutuwar tsohon Janar na soja a hannun ƴan bindiga.

    A wata sanarwa da jami’in yada labarai na rundunar, Laftanar Kanal Aliyu Danja, ya fitar ranar Litinin, ya bayyana cewa an fara wannan farmakin mai taken 'Operation Clean Sweep III' domin fatattakar ƴan bindiga a ƙaramar hukumar Matazu da wasu yankunan Katsin.

    Ya ce sun fara wannan farmaki ne tun ranar 14 ga watan Yunin 2026.

    Army

    Asalin hoton, Army/X

    Rundunar ta ƙaddamar da hare-haren ne ƙarƙashin Operation Fansan Yamma da ke aiki a yankin Arewa maso yammacin ƙasar.

    Sanarwar ta ce an samu nasarori musamman a yankunan tsaunukan Dikkawa da sauran ƙauyukan da ke kusa.

    Army

    Asalin hoton, Army/X

    Ta ce ta kai samamen ne a yankunan Adua, Nasarawa da Karaduwa, inda ya kai ga gano da lalata maboyar ‘yan ta’adda, wuraren ajiye kayayyaki da sauran cibiyoyin da suke amfani da su.

    "A lokacin harin, an lalata maɓoyar ƴan ta'adda da kayayyakinsu da motocinsu, kuma hakan ya rage musu ƙarfin kai hari a yankin," in ji sanarwar.

  5. Mustapha Kwankwaso

    Asalin hoton, Saifullahi Hassan/FB

    Jam'iyyar NDC ta tsayar da Mustapha Rabi'u Kwankwaso a matsayin mataimakin ɗan takarar gwamnan Kano.

    Ɗan takarar gwamnan Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo ne ya sanar da cewa NDC ta tsayar da ɗan Kwankwaso, a matsayin mataimakinsa a zaɓen 2027.

    Mustapha Kwankwaso ya riƙe muƙamin kwamishinan wasanni a 2023 kafin daga baya ya ajiye muƙamin a 2026.

    Hadimin Kwankwaso, Saifullahi Hassan ne ya sanar da matakin a shafinsa na Facebook.

    An ce an yanke matakin ne bayan wata ganawa ta musamman da masu ruwa tsaki da aka gudanar.

  6. Kotu ta umurci INEC ta soke rijistar jam'iyyar ADC

    ADC

    Asalin hoton, Atiku/X

    Wata babbar Kotun Tarayyar Najeriya ta umurci hukumar zaɓen ƙasar INEC ta soke rajistar jam’iyyar adawa ta ADC da wasu jam’iyyu huɗu.

    Kotun da ke Abuja ta ce jam'iyyun sun gaza cika sharuɗan da kundin tsarin mulkin kafa jam’iyyun siyasa.

    Mai Shari’a Peter Lifu ne ya yanke hukuncin, inda ya ce jam’iyyun ba su samu kashi 25 cikin 100 na ƙuri’un da doka ta tanada a zaɓukan da suka gabata ba.

    Jam’iyyun da hukuncin ya shafa su ne ADC, Accord, AA, APP da ZLP. Ya bayyana cewa jam'iyyun taka sashe na 225 na kundin tsarin mulkin Najeriya.

    Kotun ta kuma umarci INEC da kada ta bari jam’iyyun su shiga zaɓuka masu zuwa, ciki har da babban Zaɓen 2027, matuƙar ba su cika sharuɗan da doka ta tanada ba.

    Wata ƙungiyar tsofaffin ƴan majalisa ta shigar, inda ta yi zargin cewa jam’iyyun sun kasa cika ƙa’idojin da suka shafi samun goyon baya da kuma sakamakon zaɓe.

    Sai dai jam'iyyar ADC ta fitar da sanarwar cewa za ta shiga zaɓen 2027 kuma tana kira ga mabiyanta da su yi watsi da hukuncin.

  7. Ƙasashen duniya na murna da yarjejeniyar Amurka da Iran

    Kasashen duniya sun yi murna da yabawa sanarwar da Amurka da Iran suka fitar kan cewa sun amince su yi aiki da kudirin yarjejeniyar kawo karshen yakin da suke yi.

    China da Saudiyya da Kuwait sun yi maraba da yarjejeniyar wanda ake kyautata zaton za ta kawo zaman lafiya mai dorewa.

    Burtaniya da Faransa da Jamus da Italiya sun ce wannan dama ce ta daidaita tattalin arzikin duniya.

    Farashin mai ya yi saukar da aka jima ba a gani ba tun fara yakin, inda ake saida gangar danyen mai kan dala tamanin da uku zuwa da hudu.

  8. Za a dakatar da yaƙi tsakanin Hezbollah da Isra'ila a cikin yarjejeniyar Amurka da Iran

    Akwai batun dakatar da yaƙi tsakanin Hezbollah da Isra'ila a Lebanon a cikin yarjejeniyar Amurka da Iran suka cimma.

    Shugaban Lebanon Joseph Aoun ya ce yarjejeniyar za ta taimaka wajen kawo karshen yaƙin.

    Sai dai matakin na shan gagarumar suka daga manyan yan siyasar Isra'ila.

    Amurka da babbar kawarta a yankin gabas ta tsakiya ba sa tare a wannan yarjejeniyar, inda Isra'ilar ta ce ba a tuntubeta ba kafin a cimma yarjejeniyar tsakanin Amurka da Iran.

    Ministan kudi na Isra'ila ya ce wannan mummunan lamari ne ga Isra'ila da duniya baki daya.

    Shima ministan tsaron Isra'ila ya ce dakarunsu ba za su janye daga yankunan kudancin Lebanon da suka ƙwace ba duk da yarjejeniyar.

  9. Macron zai tattauna da Trump a taron G7

    Macron and Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Macron na Faransa ya ce zai yi tattaunawa mai muhimmanci da Donald Trump na Amurka a taron kasashe masu karfin tattalin arziki wato G7 da za a fara yau birnin Evian.

    Shugaba Trump ya sha barazanar ƙaƙaba harajin kashi dari kan abubuwan sha da barasa na Faransa idan har ƙasar ba ta janye harajin da take karba wajen manyan kamfononin fasahar zamani na Amurka ba.

    Shugaba Macron ya ce harajin wani ɓangare ne na dokokin Faransa da Turai, ba abinda Amurkar za ta yanke hukunci akan sa ba ne.

    A shekarar 2019 ne Faransa ta sanya haraji kashi uku cikin dari na kudaden da manyan kamfanonin fasahar zamanin ke samu.

  10. Sojojin Najeriya sun kama ƴan ƙasashen wajen 46 a wani aikin samar da tsaro

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Sojojin Najeriya sun sanar da kama ƴan ƙasashen waje 46 a wani aikin samar da tsaro da suka gudanar a jihar Ogun da ke yankin kudu maso yammacin ƙasar.

    A cewar rundunar, an kai samamen ne a ranar Alhamis a yankunan Ijebu Imushin da Ijebu Ilese tare da wasu ƙauyuka da ke kusa, bayan samun bayanan sirri masu muhimmanci.

    Mai magana da yawun rundunar, Idereghi Samuel Akari, ya ce binciken farko ya nuna cewa mutanen sun shafe kusan watanni shida a Najeriya ba tare da takardun izinin zama ba.

    Ya ƙara da cewa mutanen sun shaida wa jami’an bincike cewa su ‘yan kasuwa ne da ma’aikata masu alaƙa da kamfanin QNET, wani kamfanin sayar da kayayyaki ta intanet mai hedikwata a Hong Kong.

    Sai dai kamfanin QNET ya sha fuskantar zarge-zarge a Najeriya, inda hukumomi ke danganta kamfanin da damfara da safarar mutane da kuma shigo da mutane ba bisa ƙa’ida ba amma kuma kamfanin ya musanta hannu a irin waɗannan ayyuka, yana mai cewa yana nesanta kansa da masu amfani da sunansa wajen aikata laifi.

    Kamen na zuwa ne a daidai lokacin da ake ƙara nuna damuwa a yammacin Afirka kan wasu ƙungiyoyin da ake zargi da amfani da sunan kamfanin wajen yaudarar mutane da alƙawuran samun aiki a ƙasashen waje da kuma samun kuɗi cikin sauƙi.

    Daga cikin mutanen da aka kama, guda 18 ‘yan ƙasar Burkina Faso ne, 23 kuma daga Ivory Coast, huɗu daga Togo yayin da kuma mutum ɗaya daga Senegal ne.

    Daga bisani, an miƙa waɗanda aka kama ga Hukumar Shige da Fice ta Najeriya domin ci gaba da bincike.

  11. Za mu iya sayar da manmu ba tare da wata matsala ba - Iran

    ....

    Asalin hoton, IRNA

    Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran, Esmail Baghaei, ya bayyana cewa idan an sa hannu kan yarjejeniyar Iran da Amurka, Iran za ta fara sayar da man fetur da kayayyakin sinadarai da sauran kayayyakin mai ba tare da wata tangarda ba.

    Baghaei ya ce batun shirye-shiryen nukiliyar Iran bai shiga cikin yarjejeniyar ba, amma za a fara tattaunawa a kansa washegarin da aka kulla yarjejeniyar.

    Ya jaddada cewa har yanzu ba a tattauna cikakkun bayanai ba, amma matsayar Iran a kan shirin nukiliyarta a bayyane yake, inda ya ce:

    "Dage dukkan takunkumai, ciki har da na farko da na biyu, da na Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, da kuma wadanda suka shafi Hukumar IAEA na daga cikin batutuwan da za a tattauna washegari bayan sanya hannu, kuma ana sa ran a cimma matsaya cikin kwanaki 60."

    Har ila yau, ya bayyana cewa sakin kadarorin Iran da aka toshe a ketare, da kuma gyaran asarar tattalin arziki suna daga cikin muhimman batutuwa, yana mai cewa ɓangaren Amurka ya yi alkawarin ɗaukar matakai a wadannan fannoni.

    Baghaei ya ƙara da cewa yarjejeniyar ta kuma ƙunshi batun farfaɗo da asarar tattalin arzikin da Iran ta fuskanta.

  12. ADC ta zaɓi Amaechi a matsayin mataimakin Atiku

    ...

    Asalin hoton, Rotimi Amaechi/X

    Jam’iyyar haɗaka ta ADC ta zaɓi tsohon gwamnan jihar Rivers kuma tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa tare da Atiku Abubakar gabanin zaɓen 2027.

    Jam’iyyar ta bayyana haɗin nasu a matsayin “tikitin haɗin kai da ceto ƙasa.”

    Sakataren yaɗa labarai na ƙasa na jam’iyyar, Mallam Bolaji Abdullahi ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar inda ya ce an zaɓi Amaechi ne bayan shawarwari masu zurfi da shugabannin jam’iyya da masu ruwa da tsaki.

    Ya ƙara da cewa Amaechi ya samu goyon baya sosai a zaɓen fidda gwani inda ya zo na biyu, kuma yana da ƙwarewa a harkokin gwamnati.

    Jam’iyyar ta ce gogewar Amaechi a fannoni daban-daban na sanya shi cikin sahun manyan ‘yan siyasa masu cikakken ƙwarewa.

    Ta ce wannan gogewa za ta taimaka wajen ƙarfafa jagorancin Atiku da kuma faɗaɗa tasirin jam’iyyar a faɗin ƙasar.

    ADC ta kuma bayyana cewa haɗin Atiku da Amaechi zai haɗa yankuna da al’umma daban-daban a Najeriya.

  13. Isra’ila ta soki yarjejeniyar Iran da Amurka, ta ce barazana ce ga tsaro

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Isra’ila ta soki yarjejeniyar fahimta da aka cimma tsakanin Iran da Amurka, tana mai cewa yarjejeniyar na iya zama barazana ga tsaronta da kuma zaman lafiyar yankin.

    Yayin da wasu ƙasashe suke maraba da yarjejeniyar, jami’an gwamnatin Isra’ila sun bayyana rashin amincewarsu da ita, suna masu cewa ba za ta magance barazanar da suke ganin Iran ke haifarwa ba.

    Amma kuma firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu bai fito da martani a hukumance ba.

    Ministan tsaron cikin gida, Itamar Ben-Gvir, ya ce Isra’ila ba ta da wani wajibi na bin yarjejeniyar, yana mai jaddada cewa ƙasar mai cin gashin kanta ce.

    Ya ƙara da cewa ba za su amince da duk wata yarjejeniya da ba ta tabbatar da tsaron Isra’ila ba, yana mai cewa dole ne a lalata Hezbollah gaba ɗaya kuma ba za su janye daga yankunan da suka ƙwace ba.

    Haka kuma Ministan kuɗi, Betzalel Smotrich, ya soki yarjejeniyar yana mai cewa ba ta da amfani ga Isra’ila da sauran ƙasashen duniya masu ‘yanci.

    Ya ce dole ne Isra’ila ta ci gaba da neman hanyoyin da za ta hana Iran mallakar makamin nukiliya tare da ƙoƙarin kifar da tsarin mulkin ƙasar.

  14. Sojoji sun ƙaddamar da wani gagarumin aikin soji a Katsina bayan mutuwar Janar Rabe

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Hedkwatar Tsaron Najeriya ta ƙaddamar da wani sabon gaggarumin aikin soji da ta yi wa laƙabi da Operation Clean Sweep III a ƙaramar hukumar Matazu da ke jihar Katsina domin yakar ƴan ta’adda da ƴanbindiga.

    An fara wannan gaggarumin aiki ne bayan mutuwar tsohon Manjo Janar Rabe Abubakar mai ritaya, wanda ya mutu a hannu yanbindigar da suka yi garkuwa da shi da matar shi.

    Hedkwatar ta ce dakarunta sun fara aikin ne a ranar 14 ga Yuni 2026, domin kamo waɗanda suka aikata laifin tare da rushe hanyoyin ayyukan su, da kuma dawo da tsaro a yankunan da abin ya shafa.

    Sojojin sun ce tun bayan ƙaddamar da aikin, sun gudanar da sintiri da kai hare-hare bisa bayanan sirri, da bincike a wuraren da ake zargin ƴan ta’adda na ɓoye.

    An binne marigayin Janar Rabe Abubakar a ranar Lahadi da misalin ƙarfe 6 na yamma a makabartar Gidan Dawa da ke cikin birnin Katsina.

    Rundunar ta kuma ce za su ci gaba da matsa lamba kan ƴan ta’adda har sai sun kammala manufar wannan aiki.

  15. Tambayoyi da ƙilawaƙala kan yarjejeniyar Iran da Amurka

    ....

    Asalin hoton, Reuters

    Sanarwar cimma yarjejeniyar kawo ƙarshen rikicin da ake yi tsakanin Amurka da Iran ta kasance wata kyauta ta musamman ga Donald Trump yayin da ya ke shirin yin bikin zagayowar ranar haihuwarsa - ko da yake dai rigar rashin tabbas ta ƙanannade yarjejeniyar.

    Shugaban na Amurka ya wallafa a shafinsa na kafafen sada zumunta inda ya shelanta yarjejeniyar cewa za a buɗe mashigar Hormuz inda za a ci gaba da safarar jiragen ruwa na kasuwanci kuma Amurka za ta janye takunkumin da ta ƙaƙaba.

    "A Bari man fetur ya kwarara!" Trump ya furta a ranar Lahadi.

    Ya ci gaba da bayyana cewa, saɓanin gazawar shugabannin Amurka da suka shuɗe, ya yi nasarar ƙulla "muhimmiyar yarjejeniya" da za ta samar da "zaman lafiya da tsaro a yankin baki ɗaya".

    Irin wannan iƙirarin dai ba sabon abu ba ne ga Trump. Bugun ƙirjin da ya yi game da yarjejeniyar da aka cimma a bara da ta kawo ƙarshen yaƙin Gaza wadda ya bayyana a matsayin- "zaman lafiya da zai ɗore har abada" kuma "farkon zamanin samun aminci da imanin ga Allah" - duk da cewa dai lamarin da ke ƙasa ya sha bambam da kalaman na sa.

  16. Za a gurfanar da mutum 400 a gaban kotu kan zargin aikata laifukan ta'addanci

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Aƙalla mutum 400 ne za a gurfanar a gaban Kotun Tarayya da ke Abuja a ranar Litinin din nan kan zargin aikata laifukan ta’addanci, a ɗaya daga cikin manyan shari’o’in ta'addanci da aka taɓa yi a Najeriya.

    Shari’ar na nuni da wani muhimmin mataki a ƙoƙarin gwamnati na ƙarfafa ɗaukar alhaki da kuma magance matsalar tsaro da ƙasar ke fama da ita tsawon lokaci.

    Waɗanda ake tuhuma na fuskantar zarge-zarge daban-daban da suka haɗa da kai hare-hare da tallafawa ayyukan ƙugiyoyin masu tsattsauran ra’ayi da ta'addaci.

    Wannan na zuwa ne bayan wata babbar shari’a a watan Afrilun 2026, inda aka gurfanar da sama da mutane 500 kan zargin aikata laifukan ta'addanci kuma an samu kusan 400 da laifi.

    Mahukunta sun ce wannan mataki na da nufin kammala sauran shari’o’i da kuma gurfanar da ƙarin waɗanda ake zargi domin a hukunta su.

    Najeriya na ci gaba da fama da rikicin ta’addanci na tsawon shekaru 16, wanda ya yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da raba sama da miliyan biyu da muhallansu, yayin da matsalar garkuwa da mutane ke ci gaba da ƙaruwa a sassa daban-daban na ƙasar.

  17. Farashin mai ya sauka bayan cimma yarjejeniya tsakanin Amurka da Iran

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Farashin hannayen jari ya yi tashin gwauron zabi a kasuwannin Asiya, yayin da farashin mai ya ragu, bayan sanar da cimma yarjejeniya tsakanin Amurka da Iran.

    Farashin ɗanyen man fetur na Brent ya fara sauka da kusan kashi huɗu cikin ɗari, inda ya ragu zuwa ƙasa da dala 84 kan kowace ganga.

    Farashin man ya sakko ƙasa duk da rashin ƙarin bayani kan abun da ke ƙunshe cikin yarjejeniyar, abun da ke nuna yadda 'yan kasuwa suka yi imanin cewa komi zai daidaita da zarar an sake buɗe mashigar Hormuz.

    Kafin rikicin, kusan kashi 20 cikin ɗari na man fetur da iskar gas na duniya na bi ta wannan muhimmiyar hanya da ke yankin Tekun Fasha.

    A lokacin da faɗan ya ɓarke, Iran ta kusan hana zirga-zirgar jiragen ruwa ta wannan mashiga gaba ɗaya.

  18. Rikici ya ɓarke tsakanin ‘yansanda da masu zanga-zanga kafin taron G7 a Turai

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    An samu rikici tsakanin ‘yansanda da masu zanga-zanga a dab da fara taron ƙasashen G7, inda suka gwabza a wajen hedkwatar Majalisar Ɗinkin Duniya da ke Geneva, ƙasar Switzerland.

    Rikicin ya faru ne a daidai lokacin da ake shirye-shiryen taron a birnin Évian-les-Bains na Faransa, wanda ke kusa da Geneva, inda biranen biyu ke gefen tafkin Geneva amma a ƙasashe daban-daban.

    An gudanar da zanga-zangar a ranar Lahadi ne karkashin jagorancin wata ƙungiya da ake kira “No-G7”, wadda ta haɗa ƙungiyoyi sama da 60, ciki har da masu fafutukar kare hakkin Falasdinawa da masu rajin kare haƙƙin mata da kuma masu kare muhalli

    Masu zanga-zangar sun jefa kwalabe da duwatsu da kuma gurneti masu ƙara ga jami’an tsaron, yayin da ‘yansandan suka mayar da martani ta hanyar amfani da hayaƙi mai sa hawaye da kuma ruwan zafi wajen tarwatsa su.

    Rahotanni sun ce an kai hari kan wasu gine-gine a yayin rikicin, abin da ya ƙara nuna tashin hankali a yankin.

    Ana sa ran shugabannin ƙasashen G7 da dama za su sauka a filin jirgin saman Geneva kafin su wuce Évian ta cikin tafkin Geneva domin halartar taron.

    Jami’an tsaro na yin shiri ne don tinkarar zanga-zanga makamanciyar wadda aka fuskanta shekaru 23 da suka wuce.

    Haka kuma, babban asibitin birnin ya fara shiri na musamman domin karɓar mutane da ka iya jikkata, inda aka kafa tantuna na wucin gadi domin jinyar gaggawa.

  19. Birtaniya, Faransa, Jamus da Italiya sun yi maraba da yarjejeniyar Iran da Amurka

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Birtaniya, da Faransa, da Jamus da Italiya sun fitar da sanarwar haɗin gwiwa inda suka yi maraba da yarjejeniyar, suna masu cewa sake buɗe mashigar Hormuz abu ne mai matuƙar muhimmanci.

    Sanarwar ta kuma jaddada cewa bai kamata Iran ta taɓa mallakar makamin nukiliya ba.

    Kasashen huɗu na Turai sun ce a shirye suke su ɗage takunkuman da suka sanya wa Iran din idan har ta ɗauki matakai bayyanannu da za su ba da damar bibiyar shirinta na makamashin nukiliya don tabbatar da cewa ba ta sauka daga layi ba.

  20. Iran da Amurka za su rattaɓa hannu kan yarjejeniya ranar Juma'a a Switzerland

    .....

    Asalin hoton, BBC collage/getty/IRNA

    Iran da Amurka sun sanar da cewa sun cimma wata yarjejeniyar fahimtar juna domin kawo ƙarshen yaƙin da ke tsakaninsu, bayan watanni na rikici da tattaunawa.

    Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana a wani saƙo cewa yarjejeniya da Iran “ta kammala gaba ɗaya,” yana mai taya kowa murna kan wannan ci gaba.

    Shi ma firaministan Pakistan, Shahbaz Sharif, ya sanar cewa an cimma wannan yarjejeniya, tare da ƙara da cewa za a yi bikin rattaba hannu a hukumance ranar Juma’a, 19 ga watan Yuni, a ƙasar Switzerland.

    Haka zalika, Majalisar Tsaron Ƙasa ta Iran ta tabbatar da cewa an cimma wannan yarjejeniyar fahimtar juna da nufin kawo ƙarshen yaƙin da aka ɗauki watanni ana yi inda ta ce za a dakatar da dukkan ayyukan soja nan take a dukkan wurare.

    Wannan yarjejeniya na daga cikin manyan matakai da ake ganin za su iya rage tashin hankali a yankin Gabas ta Tsakiya tare da buɗe hanya ga zaman lafiya mai ɗorewa.